27 Afirilu 2020 - 07:27
​Iran Da UAE Sun Tattauna Kan Batutuwa Da Suka Shafi Gabas Ta Tsakiya

Ministocin harkokin wajen kasashen Iran da hadaddiyar daular larabawa UAE, sun tattauna ta wayar tarho kan muhimman batutuwa da suka shafi yankin gabas ta tsakiya, da kuma batun yaki da corona.

(ABNA24.com) Ministocin harkokin wajen kasashen Iran da hadaddiyar daular larabawa UAE, sun tattauna ta wayar tarho kan muhimman batutuwa da suka shafi yankin gabas ta tsakiya, da kuma batun yaki da corona.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a daren jiya Muhammad Jawad Zarif ministan harkokin wajen kasar Iran, tare da takwaransa na UAE Abdullah Bin Zayed Al Nahyan, sun tattauna ta wayar tarho, dangane da batutuwa da dama da suka shafi yankin gabas ta tsakiya, da kuma yadda ya kamata a tunkare su.

A yayin tatatunawar tasu, bayan taya juna murnar shigar watan Ramadan mai alfarma da kuma fara azumi a cikin wannan wata, ministocin harkokin wajen kasashen Iran da UAE, sun jaddada wajabcin hadin gwiwa da yin aiki tare a tsakanin kasashensu, domin warware matsaloli da dama da suke addabar yankin gabas ta tsakiya.

A daya bangaren kuma sun duba batun yaduwar cutar corona a yankin, da kuma yadda ya kamata a hada karfi da karfe wajen yaki da wannan cuta domin dakile yaduwarta a kasashensu.


/129